Hukumomi a kasar Spain sun fara sassauta dokokin takaita zirga-zirga da suka sanya a kasar sakamakon annobar cutar coronavirus daga yau Litinin, inda aka bar mutane dake aiki a kamfanonin kere-kere da gine-gine suka koma bakin aiki.
Ko da yake har yanzu akwai barazanar yaduwar annobar, an bukaci kamfanonin su samar wa ma’aikatansu kayan kariya da kuma tabbatar da sun bada tazarar mita 2 a tsakaninsu.
Kasar Spain na daya daga cikin kasashen da annobar ta yi tsananin gaske, inda mutane fiye da 165,000 suka kamu da cutar, kana mutune 17,000 suka mutu. Akasarin yankunan kasar sun kasance a cikin matakan hana zirga-zirga kusan tsawon wata guda.
A jiya Lahadi Firayim Ministan kasar Pedro Sanchez, ya ce wannan annobar barazana ce, ba a bangaren tasirin da ta yi ga sha’anin lafiya kadai ba, har ma da yadda take gurgunta tattali arziki da zamantakewar jama’a.
Facebook Forum