Firai Ministan Birtaniya, Boris Johnson na ci gaba da murmurewa a gadon asibitin da yake karbar magani sanadiyyar cutar coronavirus da yake fama da ita.
Johnson na samun sauki ne a daidai lokacin da da adadin wadanda cutar ta kashe a kasar ya doshi 10,000.
Kwana biyu kenan da shugaban na Birtaniya mai shekara 55 ya kwashe bayan da aka fito da shi daga sashen ‘yan-gobe-da-nisa a asibitin St Thomas da yake karbar magani.
“Firai Minista na murmurewa sosai,” in ji wata mai magana da yawun gidan gwamnati da ke lamba 10 a titin Downing.
Sai dai labarin murmurewar Johnson ta yi hannun riga da alkaluman da ke nuna cewa kusan mutum 1,000 ke mutuwa sanadiyyar cutar ta COVID-19 cikin kwana biyu a jere.
Wannan kuma na daga cikin alkaluma mafiya muni cikin kasashen da ke fama da cutar.
Ma’aikatar lafiya a Birtaniya ta ce an samu mutuum 917 da suka mutu cikin sa’a 24, adadin da ya yi kasa da wanda aka gani a ranar Juma’a.
Hukumar lafiya ta kasa NHS, ta ce daga cikin wadanda suka mutu har da wani dan shekara 11.
Mutum 9,875 suka mutu a Birtaniya yayin da adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar ya kai 78,991 bayan da aka samu karin mutum 5,234
Facebook Forum