Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Najeriya Sun Hallaka Wani Madugun ‘Yan Bindiga A Jihar Kaduna


Jirgin Sama Na Yakin Sojojin Najeriya
Jirgin Sama Na Yakin Sojojin Najeriya

A kokarin kawar da 'yan bindiga a wasu yankunan jihar Kaduna, gwamnatin jihar ta sanar da cewa rundunar sojan Najeriya ta hallaka kasurgumin 'dan bindigar nan mai suna Buhari Alhaji Halidu. Gwamnatin jihar ta ce ana ci gaba da aikin kai hari kan 'yan bindigar a yankunan da ke fama da matsalar tsaro.

Kananan hukumomin Giwa, Birnin Gwari da Igabi dai na daga cikin masu fama da hare haren 'yan bindiga na bangaren Buharin Yadi.

Gwamnatin jihar Kaduna ta ce rundunar sojan Najeriya ce ta yi nasarar hallaka ‘dan bindigar da tawagarsa a dajin da ke kananan hukumomin Giwa a jihar Kaduna da kuma Sabuwa a jihar Katsina, kamar yadda mukaddashin kwamishinan tsaro na jihar Kaduna, Malam Samuel Aruwan ya tabbarwa Muryar Amurka.

Dama dai masana harkokin tsaro sun sha ba da shawarar a bi 'yan bindiga har mafakarsu maimakon jira sai sun kai hari, a saboda haka masani kan harkokin tsaro Manjo Janar Yahaya Shinko mai ritaya ya ce kokarin da sojojin suka yi abin a yaba ne, amma akwai sauran jan aiki a gaba saboda har yanzu akwai bukatar jami'an tsaro su yi aiki na bai-daya a jihohin da 'yan bindigar ke addaba.

Manoma a karamar hukumar Giwa irinsu malam Adamu Imani, na ganin nasarar hallaka 'yan bindiga ka iya zaburar da manoma su koma gona yin ayyukansu a yankin.

Hare-haren 'yan bindiga a wasu yankuna na jihar Kaduna dai sun takaita noma a bara, sai dai kuma ana ganin idan jami'an tsaro su ka ci gaba da maida hankali kan magance matsalar hare haren 'yan bindigar, akwai yuwuwar manoma zasu koma gona a bana.

Saurari cikakken rahoto daga Isah Lawal Ikara:

Sojojin Najeriya Sun Hallaka Kusurgumin Wani Madugun ‘Yan Bindiga A Jihar Kaduna.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:34 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG