Kwamandojin kungiyar IS a yankin Sahara da suka fada komar asakarawan jamhuriyar Nijer da takwarorinsu na Faransa sun hada da wani alkalin alkalan kungiyar mai sunan Abou Maryam alias Zaid wanda dubunsa ta cika a kauyen Ingra arewacin Yatakala da Sita Ousseini loukoumane wanda ya shiga hannu a tsakanin kauyen Lamdou da Amarsingue kusa da garin Tera.
Majiyoyin tsaron sun ayyana abin a matsayin wani abbban kamu a bisa la’akari da cewa Abou Maryam da Sita Ousseini na daga cikin kwamandojojin ‘yan ta’addan da kasar Burkina Faso ta yi shelar biyan ladar makudan kudade ga dukkan wanda ya ba da bayanan da za su taimaka a kama su sakamakon mummunar ta’asar da suka jagoranta a yankin kasashe 3.
Moustapha Abdoulaye wani mai fashin baki a kan sha’anin tsaro ya yi bayani game da tasirin da wannan cafka ka iya haifarwa a yaki da ‘yan ta’adda, inda ya ce kamun da aka yi zai yi tasiri sobada wasu yaran da su ka shiga ciki da ba su san dalilin shigar su ciki ba, za su iya mika wuya.
A yayin rawar dajin da aka kira "operation Muna Tare" da hadin gwiwar sojojin sama da na kasa da ‘yan Nijer da takwarorinsu na Faransa da suka gudanar a karkarar Dolbel karamar hukumar Bankilare a ranar 6 ga watan yuli wace ta ba da damar karkashe ‘yan ta’adda da dama, aka yi nasarar rutsawa da wadanan kwamandojin reshen kungiyar IS a yankin sahara EIGS.
Jamhuriyar Nijer da ke shan yabo daga kasashen duniya saboda dagewa akan maganar tsaro a yankin sahel, na ci gaba da samun tallafi daga abokan hulda , na baya-baya shi ne wanda kasar Egypt ta bayar a karshen mako.
Tallafin ya hada da motocin yaki samfarin BRDM-2 da kananan bindigogi kirar 1900 da AK 47 kimanin 50, da wani samfurin bindigogi masu sarrafa kansu kimanin 300 da manyan bindigogin harba roka 12 da tarin harsasai da nau’rorin hango abokan gaba kamar yadda aka ruwaito a shafin yanar gizo na ma’aikatar tsaron Nijer.
Saurari rahoton a sauti:
Dandalin Mu Tattauna