A yayin da ake cigaba da kace-nace dangane da batun yadda matsalolin tsaro ke kara ta’azzara a Najeriya, wani rahoton bincike da masana tsaro suka gudanar a cikin wata 6 na farkon shekarar nan ta 2022 ya nuna cewa akalla mutane dubu 6,998 ‘yan ta’adda suka kashe a shekarar.
Wannan kididdigar na nufin mutune akalla 37 na mutuwa a kowacce rana a hannun 'yan ta’adda a sassan Najeriya dabam-daban.
Masani a sha’anin tsaro kuma shugaban kamfanin lura da al’amuran tsaro na Beacon Consult, Dakta Kabir Adamu ne ya gabatar rahoton a wani taro da aka gudanar ta yanar gizo ranar Alhamis 28 ga watan Yuli, wanda ya samu halartar gomman mutane da suka hada da masana tsaro, 'yan jarida da manyan jami'an Najeriya daga bangarori dabam-daban.
Taron dai ya yi nazari ne a game da yadda za a nemo mafita da kuma kawo karshen matsalolin tsaro da suka ki ci suka ki cinyewa a Najeriya, musamman a yankunan arewa maso yamma, gabas da kuma tsakiya. An yi ta jan hankalin mutane musamman 'yan jarida da suka halarci taron da su rinka bada sahihan rahotanni kan batun tsaro.
Dakta Adamu ya kara da cewa kashe-kashen da aka yi a wannan shekarar sun karu matuka idan aka kwatanta da shekarar 2021 da ta gabata.
A cewar sakamakon binciken, jihohin Zamfara, Neja da Kaduna na kan gaba cikin jihohin da aka fi samun yawan kashe-kashe.
Bayan haka idan aka duba kashe-kashen da aka yi a arewacin Najeriya, kashi 86 cikin 100 ne suka rasa rayukansu sakamakon hare-haren ‘yan ta'adda a watanni 6 da aka yi binciken.
A bangaren batun yin garkuwa da mutane, arewacin Najeriya na da kaso 89 cikin 100, a cewar sakamakon binciken.
Adamu ya kara da cewa jami’an tsaro na taimakawa wajen samun karuwar hare-hare musamman ta yadda suke aikata ayyukan zalunci da cin zalin fararen hula.
Daya daga cikin mahalarta taron kuma fitacciyar 'yar jarida, Kadaria Ahmed, ta bukaci 'yan jarida su rinka yin rahotanni kan sha’anin tsaro bisa da’a da bin ka’ida.
A nasa jawabin a yayin taron, masani a harkokin tsaro, Guruf Kyaftin Sadiq Garba Shehu, ya bayyana cewa karanci isassun sojoji na daya daga cikin matsalolin da ke gurgunta kokarin kawo karshen matsalar tsaro a Najeriya.
A cewar kyaftin Garba, idan ana maganar kashe kudi gwamnatin Najeriya ta kashe kuma tana kan kashewa, amma inda gizo ke sakar shi ne inda kudaden suke shiga kuma matsalar rashin bibiyar kudaden da ake bai wa jami’an tsaron na kawo tarnaki ga samun nasara a kawo karshen rashin tsaro, ya kara da cewa ya kamata a tabbatar da inda kudin da gwamnati ke kashewa don yaki da matsalolin tsaro ke shiga, hakan zai taimaka matuka wajen samun nasara.
A wani bangare kuma, masanin tsaro Temitope Yusuf Olodo, a nasa jawabin ya bayyana cewa kawo karshen masu hannu a ci gaban matsalolin tsaro da ake gani a Najeriya na da muhimmanci wajen kawo karshen matsalolin baki daya.
Mista Temitope ya kara da cewa, rashin amfani da hanyar kawar da tsaro ta zamani na haddasa babban gibi da kawo tarnaki ga nasara, wanda dole sai gwamnati ta gyara musamman ganin cewa sojojin Najeriya na amfani da hanyar yaki da 'yan bindiga irin ta karni 19, kuma dole a canza yadda ake horas da jami’an tsaron kasar.
Kyaftan Umar Aliyu shi kuma ya bayyana rashin tsaro a matsayin saniyar tatsa, inda ya ce mutane da kungiyoyi na amfani da matsalar musamman a arewacin Najeriya a matsayin hanyar samun kudi masu kauri, wanda ya zama wajibi a bada kulawa ta musamman wajen kawo karshen hakan.
Dan gwagwarmaya mai fafutukar kare hakkin bil’adama da kuma fashin baki kan al’amuran da suka shafi al’umma Dakta Bulama Bukarti, ya bayyana cewa kungiyoyin ta’addanci na da sansanoni a sassan Najeriya dabam-daban, al'amarin da ya kamata a mayar da hankali a kai.
Haka kuma, Bukarti ya ce yadda kungiyoyin 'yan ta'adda ke ci gaba da bude sansanoni a wurare da dama musamman ma inda a baya babu, ya zama dole gwamnatin kasar ta yi duk mai yiwuwa wajen ganin an kawar da su a duk fadin kasar don samun ci gaba mai dorewa.
A halin da ake ciki, matsalolin tsaro na kara ta'azzara a Najeriya inda a baya-bayan nan 'yan ta'adda suka kai hare-hare a Abuja babban birnin tarayyar kasar, ciki har da farmakin kan gidan gyara hali na Kuje, da hari kan shingen sojoji da aka kafa a kusa da makarantar koyon aikin lauya ta Bwari, da kuma harin da aka kai a daren Alhamis a kan hanyar Madalla da ke tsakanin Abuja da jihar Neja.