Jiragen Yakin Najeriya da Nijar karkashin rundunar kawancen kasashen yankin tafkin Chadi, sun kai farmaki ba tare da kakkautawa ba akan mayakan Boko Haram a arewacin jihar Borno, da yankin tafkin Chadi.
Wannan sabon farmakin dai ya biyo bayan Tsattsauran matakin da kasashen yankin suka dauka na kawo karshen aika aikar kungiyoyin ta'addanci a yankin, al'amarin da ya sa aka kaddamar da wannan artabu mai taken "Operation 'Yancin Tafkin."
Tun farkon makon nan ne aka tsananta kai hare haren musamman ma shekaran jiya, da jiya da yau inda dakarun suka tottoshe yankunan da 'yan ta'addan ke kai komo a tsakanin kan iyakar Najeriya da Nijar, a daya bangaren kuma ana ci gaba da yi masu barin wuta bayan an takurasu,
Kakakin Rundunar sojojin saman Najeriya, Air Commodore Ibikunle Daramola, ya shaidawa Muryar Amurka cewa jiragen saman leken asiri da kuma jiragen yakin Najeriya da Nijar na rugurguza 'yan ta'addan yayin da a daya bangaren kuma jiragen yakin ke marawa dakarun da ke kasa wurin ci gaba da kai farmakin.
Ganin a baya dakarun kawancen sun kaddamar da farmakin Operation Gama Aiki, a yankin tafkin Chadi, wakilin Muryar Amurka ya tambayi kakakin rundunar sojojin saman ko menene banbancinsa da wannan sabon farmakin? Sai Air commodore Daramola yace wannan farmakin na Operatin yancin tafki wani yunkuri ne da aka tsara shi a tsanake don ganin bayan 'yan ta'addan.
Ko a makon da ya gabata ma, sai da dakarun kawance kasashen yankin tafkin Chadin suka afkawa 'yan ta'addan inda a karon farko suka kashe manya manyan mayakan 'yan ta'addan guda arba'in.
Ga karin bayani cikin sauti.
Facebook Forum