A Najeriya Kungiyoyi masu zaman kansu 13 ne suka yi zangazangar kalubalantar Hukumar Zabe akan Zabukan Gwamnoni da ba a kamalla ba, inda suke ganin akwai lauje cikin nadi.
Wannan Zangazangar na zuwa ne a daidai lokacin da Hukumar Zabe ta ayyana ranar 23 ga wannan wata a matsayin ranar da za maimaita zabe a wasu mazabu na jihohi 6 a kasar.
Kungiyoyin sun yi tattaki zuwa Hukumar Zaben inda suka kai kukansu a game da yadda aka gagara kammalla zabukan, kamar yadda daya daga cikin shugabanin Kungiyoyin Mohammed Aminu, ya bayyana inda ya ce sun kawo takarda a rubuce, kuma a ciki suna rokon Hukumar Zabe da ta yi kokarin aiwatar da aikin za6en cikin gaskiya ba tareda tauye wa al'umma hakinsu ba.
Kuma suna ganin idanun duniya na kan Hukumar Zaben akan wadanan za6ukan Gwamnonin.
Shugaban tsaro na Hukumar Zaben Kelechi Maduneme yace Hukumar za ta duba koken Kungiyoyin da idanun basira tareda tabbatar masu cewa Hukumar za ta yi aikin ta babu sani babu sabo domin tana bin dokokin da aka gindaya a dokar zabe.
Bayanin da Shugaban tsaro na Hukumar zaben Kelechi ya yi ya sa daya daga cikin 'yan Kungiyar Tijjani Abdulmumuni ganin cewa lallai ya kamata su matasa su goyi bayan Hukumar zaben, domin ta ayyanna gaskiya saboda a samu cigaba a kasar.
Ga rahoton wakiliyar mu Medina Dauda daga Abuja Najeriya.
Facebook Forum