Hukumar dake kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya tace harin da 'yan Boko Haram suka kai Bosso cikin jihar Diffa dake jamhuriyar Nijar ranar Juma'ar da ta gabata wanda ya tilastawa sojoji ficewa daga garin ya haifar da fargaba a kawunan jama'a da yanzu suka tagayyara.
Yawancinsu sun tsere neman mafaka a garuruwan dake bangaren yammacin kasar irin su Tumur. Mutane sun kuma shiga rudani bayan da wasu rahotanni suka ce mayakan Boko Haram sun kwace ikon garin Bosso. Daga baya ne sojojin gwamnati suka bayar da sanarwar alamuran garin sun dawo hannunsu.
A wata sanarwa da gwamnatin Nijar ta bayar bayan zaman majalisar ministocin kasar, ta bayyana shirin daukan matakan gaggawa domin tallafawa bayin Allah da suka tagayyara wadanda aka kiyasta yawansu sun kai dubu hamsin.
Kazalika hukumomin Nijar sun nemi aminan kasashe da kungiyoyin kasa da kasa su taimaka.
Asumana Malam Isa kakakain gwamnatin Nijar yace a cikin sanarwar sun fada Bosso tana hannun sojojin kasar kuma an kara yawan sojojin garin. Yace gwamnati da masu hannun da shuni zasu dauki karfafan matakan kai wa wadanda suka bar gidajensu doki.
Tuni dai kungiyar agaji ta kasa da kasa ko Red Cross ta bayyana cewa ta tanadi tallafi domin 'yan gudun hijira saidai akwai bukatar daukan matakan tsaron jami'anta kamar yadda jami'in hulda da jama'a na kungiyar Dabi Umaru ya bayyana. Yace dole a tattauna da gwamnati a san jihohin da 'yan gudun hijiran suke domin su samu izini da kariya kafin su kai agaji.
Ga karin bayani.