Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Isra'ila Sun Kaiwa Sansanin Sojan Syria Hari


Syria
Syria

Rundunar sojan Syria tace jiragen saman yakin Isira’ila sun kaiwa wani sansanin sojan ta hari da sanyin safiyar yau Alhamis, kusa da garin Masyat, harma suka kashe sojoji guda biyu da yin barna.

Sanarwar ta sojojin, tace sojojin Isira’ila sun harba makamai masu linzami daga sararin samaniyar kasar Lebanon. Garin Masyat yana lardin Hama kusa da tekun maditareniyan kimamin kilomita arba’in arewa da kan iyakar Syria da Lebanon.

Rundunar sojan ta Syria tayi kashedin irin barazanar da irin wannan tsokana ka iya hadasawa tsaro da kwanciyar hankali a yankin.

Rundunar sojan Isira’ila , bata ce uffan ba gameda wannan hari. Galibi bata fadin komai idan ta kai irin wannan harin. To amma, a baya, jami’an Isira’ila sun tabbatar cewa hare haren da sojojin kasar ke kaiwa cikin Syria suna auna wuraren da suke zargin Syria tana adana makaman da zata yi jigilar su, ga kungiyar Hezbollah da cibiyar ta ke cikin Lebanon.

Mayakan Hezbollah suna fafatawa a cikin Syria domin goyon bayan shugaba Bashar Al Assad.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG