Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Congo Sun Dakile Wani Yunkurin Juyin Mulki


Tshisekedi
Tshisekedi

A watan Disamba ne aka sake zaben Tshisekedi a matsayin shugaban kasa a wani zabe mai cike da rudani, wanda ‘yan adawa ke neman a soke shi.

Sojojin Congo sun ce sun dakile wani yunkurin juyin mulki da safiyar Lahadi tare da kame wadanda suka kai harin, ciki har da wasu 'yan kasashen waje, biyo bayan hare-haren da aka kai a fadar shugaban kasa da kuma gidan wani na hannun daman shugaban Congo wanda ya yi sanadin mutuwar mutane uku a Kinshasa babban birnin kasar.

Da farko kafofin yada labaran cikin gida sun bayyana mutanen da ke dauke da makamai sojojin Congo ne amma sai suka bayar da rahoton cewa suna da alaka da ‘dan adawar kasar Christian Malanga da ya yi gudun hijira, wanda daga baya ya sanya wani faifan bidiyo a Facebook yana yi wa shugaba Felix Tshisekedi barazana.

An kashe Malanga ne a fadar shugaban kasa bayan ya bijire wa kamun da masu gadi suka yi masa, mai magana da yawun sojojin Congo Brig. Janar Sylvain Ekenge ya shaidawa Kamfanin Dillancin Labarai na Associated Press.

A watan Disamba ne aka sake zaben Tshisekedi a matsayin shugaban kasa a wani zabe mai cike da rudani, wanda ‘yan adawa ke neman a soke shi.

Kasar wacce ke tsakiyar Afrika ta sha fuskantar irin wannan yanayi na zabuka masu cike da takaddama a baya.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG