Wannan dai shi ne al’amari na baya-bayan nan a cikin watanni da aka kwashe ana zaman dar-dar tsakanin 'yan tawayen da ke samun goyon bayan Iran da Amurka.
Rundunar sojin Amurka ta ce jiragen da aka lalata da safiyar ranar Asabar, sun yi barazana ga sojojin Amurka da na hadin gwiwa da kuma jiragen ruwan 'yan kasuwa a yankin.
"Wadannan ayyuka sun zama dole don kare sojojin mu, tabbatar da 'yancin zirga zirga, da kuma tabbatar da tsaro ga Amurka, haɗin gwiwa, da jiragen ruwa na 'yan kasuwa," in ji CENTCOM.
Babu wani bayani daga 'yan tawayen Houthi, wadanda ke iko da yawancin arewaci da yammacin Yemen.
'Yan tawayen sun kaddamar da hare-haren jiragen sama marasa matuka da makamai masu linzami kan jigilar kayayyaki a tekun na Bahar Ahmar a cikin watan Nuwamba. Sun kuma harba makamai masu linzami zuwa Isra'ila, ko da yake sun gaza ko kuma an tare su.
'Yan tawayen dai sun bayyana yakin nasu a matsayin wani yunkuri na tursasawa Isra'ila ta kawo karshen yakin da take yi da kungiyar Hamas a zirin Gaza.
'Yan Houthi dai sun ci gaba da kai hare-hare duk da sama da watanni biyu na hare-haren da Amurka ta ke kai masu.
Dandalin Mu Tattauna