A Afirka ta kudu, 'yan kasar suna bayyana rashin amincewa da shirin karawa shugaban kasar Jacob Zuma albashi, matakin da zai fara aiki daga watan gobe, kamar yadda wani dan majalisar kasar daga bangaren 'yan hamayya Jordan Lewis na jam'iyyar Democratic Alliance, yayi bayani.
Daga watan gobe, shugaba zuma zai rika karbar
Dalar Amurka dubu 188,000 ako wace shekara, kamar yadda wata hukumar da take duba albashin manayan jami'an gwamnati ta bada shawarar a karawa shugaban albashi da kashi biyar cikin dari. Haka nan dukkan ma'aikatan gwamnati zasu sami karin kashi biyar cikin dari kan alabashinsu a shelarar kudi bana.
Amma wasu 'yan hamayya da kungiyoyin farar hula, suka ce shugaba Jacob zuma, bai cancanci wannan kari ba, saboda mummunar halin da tattalin arzikin kasar yake ciki.
Jam'iyyar 'yan hamayyar da ake kira DA a takaice, ta gabatar da gyare-gyarren fuska daban daban har biyu, na kin amincewa da da karin albashin shugaban kasar, amma kudurin bai kai labari ba, domin wakilai 'yan jam'iyyar ANC mai mulki sunki su goyi bayan matakin.
Dan majalisa Lewis Jordan, yace jam'iyyarsa a hukumance ta rubuatawa shugaba zuma takardar kukan kada ya amince da wannan kari. Amma magoya bayan jam'iiyar ANC suka ce shugaban ya cancani wannan kari, ganin cewa wata hukuma ce mai zaman kanta ta bada wannan shawara.