Sojojin Najeriya sun ce sun kama wasu mata uku da suke zargin cewa 'yan ta'adda ne, wadanda kuma ake zargin su na daukar mata domin su shiga cikin kungiyar.
A cikin wata sanarwar da rundunar sojojin Najeriyar ta bayar mai dauke da sa hannun Kanar Onyema Nwachukwu, an bayyana cewa sojoji sun kama hafsat Usman bako da zainab Idris da kuma A'isha Abubakar a kan hanyarsu ta zuwa garin Madagali a jihar Adamawa, daga inda suka yi niyyar shiga daji domin haduwa da 'yan'uwansu.
Sojojin suka ce Hafsat Bako, matar wani dan Boko Haram ne da sojoji suka binciki gidansa a Jimeta a shekarar 2012, suka samu bindigar AK-47 da kunshin harsasai biyu. Ya gudu ya koma Sokoto, inda aka kashe shi lokacin wani artabu da sojoji a can.
Sojojin suka ce Hafsat Bako ita ce jagorar wadannan mata wadanda ake zargin su na kuma aikin leken asiri ma kungiyar Boko Haram.
Babu wata kafa dabam da ta tabbatar da sahihancin wadannan kalamu na rundunar sojojin ta Najeriya.