Tun da farko dai 'yan bindigar, kamar yadda wata majiya ta shaidawa VOA, sun taru ne a kauyen Madada da ke cikin yankin karamar hukumar Maru da nufin kai harin ta'addanci a wasu yankunan jihar kebbi.
Bayan da 'yan ta'addan suka sami labari sojojin kasa sun masu kwanton bauna ne kuma su ka juyo, inda kuma wasu jiragen yakin kasar suka yi masu ruwan wuta.
Kakakin rundunar sojojin saman Najeriya Air Commodore Edward Gabkwet ya shaidawa muryar Amurka cewa ba shakka sun hallaka dandazon yan bindiga masu yawan gaske, duk da yaki ya bayyana ainihin adadin wadanda su ka hallaka.
Ya ce ba kome suke bayyanawa a fili haka sakaka ba, amma dai harin ya sami cikakkiyar nasara sosai.
Mutanen da ke wannan yanki kuma tuni suka nuna farin ciki bisa yadda suka ce a baya-bayannan jami'an tsaron na taka rawar gani sosai, inda suka yi fatan hakan zai ci gaba.
Rundunar sojojin saman ta ce tana da kwarin gwiwar wannan hari zai taimaka gaya wajen kara dakile kaifin aika-aikar yan bindigar.
Saurari rahoton:
Dandalin Mu Tattauna