A wani mataki na aiki da cikawa, kakakin rundunar mayakan saman Najeriya, Air Commodore Edwad Gabkwet, a cikin wata sanarwa da ya sanyawa hannu, ya ce jiragen yakin Najeriya da ke aiki a karkashin rundunar OPERATION HADIN KAI a arewa maso gabas ta kai wani mummunan farmaki a Arina Woje, wurin dake zaman matattarar 'yan ta'adda.
Air Commodore Gabkwet ya ce Arina Woje wuri ne dake kudancin Tumbuns a kusa da tafkin Chadi da 'yan ta'adda ke amfani da shi a matsayin wurin jinyar mayakansu da aka raunata kana su ke kuma jibge dimbin makamansu.
Sojojin saman Najeriya sun kai hari a wannan wuri a ranar goma sha uku ga watan Yunin wannan shekara, abin da ya sa 'yan ta'addan su ka yi kaura biyo bayan zafafa kai hare-hare.
Bayan tantance bayanan sirrin da aka samu an bai wa jiragen yakin izinin kai farmaki inda suka fata fata. Sahihan bayanan sirri sun tabbatar da irin mummunar barnar da aka yi wa 'yan ta'addan a wannan wuri.
Bugu da kari, sojojin saman sun kuma kai farmaki Bille da ke karamar hukumar Degema a jihar Rivers, inda dama ya yi kaurin suna wajen sata da tace danyen mai ba bisa ka'ida ba. Bayan dai gano yadda 'yan ta'addan ke tace man sannan aka ga ma'ajiya da tankoki makare da haramtaccen mai da aka tace, take jirgin yakin mayakan saman ya afkawa wannan waje inda ya ragargaza shi.
Kakakin sojojin saman yace ana kai hare-haren ne da zummar hana miyagun sakat a kuma rusa tare da bata iya man da ko dai suka sace ko suka adana, wanda wannan aiki nasu ya yi wa muhalli da tattalin arziki illa ba kadan ba.
An dai sami cikakkiyar nasara a yayin wannan hari ta sama, abin da ya sa hedkwatar rundunar sojojin saman Najeriya shan alwashin ci gaba da aiki kafada da kafada da sauran jami'an tsaro wajen tabbatar da tsare, da kuma samar da tsaro a duk sassan da ke fuskantar duk wata barazanar tsaro.
Saurari rahoton cikin sauti:
Dandalin Mu Tattauna