Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Siyasar Ubangida Na Dakile Ci Gaban Dimokradiyya - El-Jibril Doguwa


Taron gangamin yakin neman zabe
Taron gangamin yakin neman zabe

Siyasar ubangida, siyasar kudi da amfani da kayayyakin masarufi domin jan hankalin masu kada kuri’a na daga cikin manyan al’amura da manazarta kan harkokin siyasa ke cewa suna dakushe ci gaban dimokaradiyya a Afrika da sauran kasashe masu tasowa, irin su Najeriya.

A Najeriya, siyasar ubangida na tasiri matuka ga sha’anin zabe musamman na fidda gwani, amma Dr. Sa’idu Ahmad Dukawa masanin kimiyyar siyasa a Jami’ar Bayero da ke Kano, yace ko da yake a jamhuriya ta daya akwai yanayi ko tsarin siyasar ubangida a Najeriya, amma ba irin na yanzu ba ne. Kamarsu Malam Aminu Kano da Sardaunan Sokoto, da duka iyaye na siyasa sukan bada umarni a bi, amma sun tafiyar da jagoranci bisa akida da nusar da magoya baya.

To amma a cewar, Sanata Mas’ud El-Jibril Doguwa, tsohon wakilin mazabar Kano ta kudu a majalisar dattawan Najeriya, gwamnonin kasar su ne tushen matsalar siyasar ubangida, yana mai cewa sun dakile ci gaban dimokaradiyya a Najeriya ta hanyar makure wuyan kananan hukumomi da majalisun dokoki na jihohinsu.

"Ba sa bari harkokin mulki su gudana a kananan hukumomi, ba sa barin ‘yan majalisar dokoki su gudanar da ayyukansu yadda ya kamata, kuma basa bari a yi zaben cikin gida na jam’iyyu bisa ka’idar zabe, sai dai suyi abin da ake kira dauki dora a yayin fitar da ‘yan takara," a cewar Doguwa.

Watakila hakan ce ta sanya masana kimiyyar siyasa ke cewa akwai alaka ta kud-da-kud tsakanin siyasar uban gida da siyasar kudi wadda kan rikide ta haifar da yanayin amfani da kayayyakin masarufi domin jan hankalin masu zabe.

Sai dai ana ci gaba da mahawara a tsakanin manazarta kan cewa ta yuwu sauya fasalin wasu daga cikin takardun kudin Najeriya ka iya tasiri ta wannan fuska, amma Dr. Dukawa ya ce sauya fasalin takardun kudin ka iya rage amfani da kudi a zabe, amma akwai rahotannin da ke cewa ‘yan siyasa sun sayi kayayyakin masarufi domin raba wa masu zabe.

Masana ilimi kimiyyar siyasa sun ce sayan kuri’a karkashin tsarin siyasar ubangida na nufin tafka magudin zabe.

Shin ko gwamnoni kan taka rawa a nan? Sanata Mas’ud El-Jibril Doguwa ya ce gwamnoni ke daure gindin siyasar kudi a Najeriya, domin kuwa kusan dukkanin arzikin kasa na hannunsu.

Tuni dai hukumar zaben Najeriya ta INEC ta ce kirkiro da na’urar BVAS na daga cikin matakan da ta dauka domin kawar da magudin zabe a kasar, kamar yadda shugaban hukumar Farfesa Mahmud Yaqub ya bayyana.

Bayan haka, su ma ‘yan kasar na bayyana ababuwan da suke fatan zasu dakile yunkurin magudin zabe, yayin da wasu ke cewa ba zasu karbi abin hasafin da ‘yan siyasa ke raba wa masu zabe ba, kawai dai zasu yi zabe bisa cancanta. Wasu kuwa na cewa zasu karba amma su zabi dan takarar daya dace.

Sakamakon wannan zaben dai shine zai tabbatar da sauyin da ‘yan Najeriya ke fatan gani a tsarin zabe kasar da kuma tasirin matakan da hukumar INEC ta bullo dasu.

Saurari rahoton Mahmud Ibrahim Kwari:

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00

XS
SM
MD
LG