An zargeta da yin anfani da wasu hanyoyin da basu kamata ba wajen karba da aika sakkoninta na email, daya daga cikin batutuwa mafi zafi da aka fi cece-kucce a kansu a lokacinda ake yakin neman zabe a bara.
Musamman Sufeto-Janar din, Michael Horowitz yace yana son ya fahimci yadda shugaban Hukumar FBI, James Comey ya gudanarda binciken da ya share shekara daya yana gudanarwa akan Hillary Clinton, wacce ta rike mukamin Sakatariyar-Harkokin-Wajen-Amurka daga 2009 zuwa 2013, kuma tayi kokarinh zama shugabar Amurka mace ta farko, abin ya gagara.
Hilary dai ta dora laifin kayen da aka yi mata zabe akan shi Comey a dalilin sanarwar da ya bada ta sake bude binciken da yake a kanta, ana saura kwannaki 11 kacal a yi zaben na Amurka, abinda wasu ke ganin wannan ne yasa ta fadi zaben kuma abin ya baiwa abokin takararta Donald Trump na jam’iyyar Republican damar lashe zaben.