A jihar Neja an gudanar da bikin baiwa sabon sarkin Borgu na goma sha bakwai Barrister Muhammad Sani Haliru Dantoro sandar girma a garin na Borgu.
Lokacin da yake baiwa sabon sarkin sandar girman gwamnan jihar Alhaji Abubakar Sani Bello ya taya sabon sarkin murna sannan ya bayyana bukatar ganin sarkin ya bada gagarumar gudummawa wajen kawo cigaban kasa da hadin kan al'umma.
Shi ma a nashi jawabi Maimartaba sarkin Kano Alhaji Muhammad Sanusi II wanda ya halarci bikin ya gabatarda wani jawabi da ya janyo hankalin shugabanni akan mahimmancin kare rayukan wadanda suke shugabanta.
Sarki Sanusi II yace kashe-kashen da ake yi suna tada hankali. Yace ita rayuwa ana kareta ne ta hanyoyi da yawa kuma amanar yin hakan ya rataya ne akan sarakuna da gwamnatoci. Sarkin ya bada misalai.
Yace barin asibitoci ba magani ko ba likitoci da barin tituna babu gyara da barin kasa babu tsaro suna cikin hanyoyi na kashe al'umma. Yace ko mutum bai kashe ba amma kuma bai dauki hanyoyi na ceton rayuwa ba to ya kashe ke nan.
Sabon sarkin Borgun, bayan ya karbi sandar girma, ya zanta da Muryar Amurka inda ya gabatar da wasu bukatu. Ya roki gwamnatin jihar ta duba matsalar rashin hanyoyi masu kyau a masarautarsa. Yayi fatan gwamnan jihar zai taimaka a gyara masu hanyoyinsu. Idan babu hanyoyi babu yadda za'a samu habakar tattalin arzikin wuri. Masu saka jari da gina masana'antu zasu guji wuraren da basu da hanyoyi masu kyau.
'Ya'yan masarautar sun kuma yi furuci akan sabon sarkin da suka samu. Barrister Na Sale yace yana farin ciki da samun sabon sarkin. Shi ma Baraden Borgu ya taya sabon sarkin murna.
Sarkin Musulmi Sultan Muhammad Sa'ad Abubakar III ya kasance wurin bikin sarautar amma jami'an tsaro da dogarawa suka yi shamakin hana manema labarai kaiga sarkin.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari da karin bayani.