Shugaban Kungiyar Izalatul Bid’a Wa’iqamatus Sunna Sheihk Abdullahi Bala Lau ya ce binciken batun jirgin saman Shugaban Kungiyar Kiristan Nijeriya (CAN), Rev. Ayo Oritsejafor da aka samu dauke da kudi mai yawa na sayo makamai, na da muhimmanci wajen tabbatar da zaman lafiya tsakanin Kirista da Musulmi.
Wakilinmu a Abuja Nasiru Adamu Elhikaya ya ruwaito Sheikh Lau na cewa ya kamata Shugaban kasa da jami’an tsaro da Majalisar Tarayya su binciko matsayin jirgin da matsayin kudin da kuma matsayin makaman. Haka kuma a binciki abin da ya sa ba a bi hanyar da aka saba bi ba wajen sayo makaman.
Ya ce ko da ma hayar jirgin aka bayar ai duk da haka jirgin mallakin mai shi ne. Saboda haka abin na da tayar da hankali in ji shi.To saidai wani Mataimakin Shugaban na CAN mai suna Rev. Shayibu Bely a ce sam Kirista ba su shirya wani makirci ga Musulmi, kuma ba su da wani makamin da ya wuce Littafi Mai Tsarki (Bible).