A kokarin da ake ci gaba da yi da nufin lalubo hanyoyin samar da zaman lafiya da tabbatar da tsaro a yankunan arewacin Najeriya masu fama da rigingimu, an yi wani taron karawa juna sani na musamman a birnin Lagos wanda ya samu halartar shugabannin jahohin na arewa masu fama da 'yan ta'adda.
A wajen taron na Lagos an tattauna batutuwa da yawa wadanda suka bayar da damar gano cewa cin hanci da rashawa ne ke hana samar da ayyukan yi ga matasa, wanda hakan kuma shi ne babban abun da ke tura matasan su na shiga ta'addanci kawai domin su samu kudaden kashewa .
Wakilin Sashen Hausa a birnin Ikko, Ladan Ibrahim Ayawa ya halarci taron kuma ga rahoton da ya aiko:
Jami'ar Colorado ta kasar Amurka da Mujallar Lead ta Najeriya, su ne suka hada guiwa suka shirya taron a birnin Ikko, wanda ya bayar da damar yin musanyar ra'ayi da wasu shugabannin jahohin Arewacin Najeriya dake fama da fitinar ta'addanci.