Jami'an tsaron da suka amsa gayyatar Majalisar sun hada da babban Hafsan Hafsoshin Sojojin Najeriya Lucky Irabor da babban Hafsan Sojojin Kasa Ibrahim Attahiru da babban Hafsan Sojojin Sama Isiyaka Amao da kuma na ruwa Auwal Gambo, sai Sufeto Janar na 'yan sanda Baba Usman da Shugaban Hukumar leken asirin Kasa Manjo Janar S.A Adebayo da kuma shugaban Hukumar tsaro na farin kaya Yusuf Bichi wadanda yan majalisar suka yi wa tambayoyi daya bayan daya a wani yunkuri na samar da tsaro a kasar.
Wanan zama shi ne na farko da Majalisar dattawa za ta yi da wadannan sababbin shugabanin.
Sanata Ali Ndume shi ne shugaban komitin kula da harkokin sojin kasa ya bayyana cewa, majalisa ta gamsu da bayanan shugabanin tsaron kuma za ta hada kai da bangaren zantaswa wajen ganin an ba su kudade da suke bukata na gudanar da aikin su. Ndume ya ce za su kar6i kwarya kwaryar kasafin kudi da ake sa ran shugaban kasa zai kawo domin a cimma burin dakile matsalar tsaron.
Najeriya na cigaba da afkawa cikin mawuyacin halin ta6ar6arewar tsaro ta yadda a kullum ana rasa rayuka da dama kuma ana sace wasu ana yin garkuwa da su, wani abu da Sanata Ibrahim Gobir ya ce ya zama kalubale ne ga yan kasa baki daya.
Gobir ya ce hakki ne akan kowanne dan kasa idan ya ga abinda ba daidai ba ya sanar da hukuma.
To sai dai ga kwararre kan sha'anin tsaro na kasa da kasa Dokta Yahuza Ahmed Getso yana ganin akwai wani abinda ake 6oyewa idan har ya zuwa yanzu Majalisa tana zaman sirri da shugabanin hukumomin tsaro.
Dokta Yahuza ya ce lokaci yayi da za a fito fili balobalo a bayyana wa 'yan kasa halin da ake ciki da kuma yawan kudaden da aka riga aka kashe a wannan harka ta tsaron kasa.
Irin wanan zama a asirce an dade ana yin sa da tsofin hafsoshin sojoji da suka shude da kuma wanan majalisa wanda har ya zuwa yanzu kokari ake cigaba da yi na samo maganin wanan barazana na sha'anin tsaro.
Saurari cikakken rahoton a sauti: