Irin wannan ya faru ne a garin Goronyo a jihar Sakkwato da ke arewa maso yammacin Najeriya, inda jama'a suka kama wasu mutane uku da ake tuhumar ‘yan bindiga ne suka cinna masu wuta suka kona su kurmus har suka mutu maimakon a mika su ga hukuma.
Da VOA ta tuntubi neman samun magana da wasu ‘yan garin wanda suka ga lokacin da abin ke faruwa kowa na tsoron fadin yadda lamarin ya wakana.
Sai muka tuntubi shugaban karamar hukumar ta Goronyo Abdulwahab Muhammad Goronyo wanda ya nuna takaici akan abin da ya faru domin ya ce an yi asara sanadiyyar kona mutanen, kamar ta rashin samun wani bayani daga gare su wanda wata kila kan iya kai ga a samun sirrin yadda ayukkan ta'addanci ke wakana a yankin.
Rundunar 'yan sanda ta jihar Sakkwato ta bakin kakakin ta ASP Sanusi Abubakar, ta tabbatar da aukuwar lamarin.
Karin bayani akan: jihar Sakkwato, Goronyo, ASP, Nigeria, da Najeriya.
Duba da cewa wannan ba shi ne karo na farko ba da hakan ya faru domin ba da jimawa ba ne aka kona wani da ake tuhumar dan ta'adda ne a garin Kware ta jihar Sakkwato.
Amma da muka tuntubi mai sharhi kan lamurran tsaro Detective Auwal Bala Durimin, a cewarsa hakan yana da illoli da dama.
Masu lura da al'amurra dai na ganin cewa yadda jama'a suka fara daukar wa kansu hukumci, akwai bukatar hukumomi su kara tashi tsaye domin samarwa kansu kima ta yadda jama'a za su yarda da ayukkansu domin kaucewa ci gaban irin wannan a gaba.
Saurari rahoto cikin sauti daga Muhammadu Nasir: