Erdogan, yayi magana ne a Istanbul a karshen taron koli da Majalisar Dinkin Duniya ko MDD ta shirya da nufin duba matsalolin 'yan gudun hijira daga kasashen Syria da Iraqi zuwa Turkiyya da kuma kasashen Turai.
Wannan gargadin da Erdogan ya bayar shine alamu na baya bayan nan na karin zaman dar-dar tsakanin kungiar tarayyar turai da Turkiyya kan yarjejeniyar da sassan biyu suka sanya hannu a kai cikin watan Maris, da yayi tanadin baiwa Turkiyya gudumawar dala miliyan dubu bakwai, idan gwamnatin kasar zata taimaka wajen hana korarar 'yan gudun hijira da kuma karbar wadanda turai ta koro su daga Girka.
Amma Turkiyya ta aza sharadi kan yarjejeniyar na baiwa 'yan kasar damar tafiya turai ba tareda neman visa ba, bukatar da shugabannin turai suka bukaci Ankara ta aiwatar da sauye saiuye ta fuskar 'yancin Dan'Adam na zummar taimakawa 'yan gudun hijira da suke kasar.