Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Nijer Ya Yi Rangadi A Kauyen Da Yan Ta'adda Suka Hallaka Mutane 69


Shugaban kasar Nijer Mohamed Bazoum ya yi rangadi a karshen mako a gundumar Banibangou don jajantawa al’umma rasuwar wasu mutane kimanin 69 cikinsu har da magajin gari wadanda ‘yan ta’adda suka yi wa kwanton bauna a farkon mako.

Shugaban ya sha alwashin kawo karshen matsalar tsaron da yace ta na hana masa barci.

Wannan rangadi dake matsayin wata hanyar isar da sakon ta’aziyar al’ummar Nijer zuwa ga ‘yan uwansu na karkarar Banibangou a daidai lokacin da suke juyayin rasuwar mutane sama da 60 wani abu ne da a daya bangare ke jaddada aniyar magance matsalar tsaro a wannan yanki dake zama mafi hadari a jihar Tilabery .

Karancin abinci da rashin tsaro sune matsalolin da shugabanin karkarar Banibangou suka gabatarwa shugaban kasa a jawabin da suka gabatar kafin daga bisani ya fadi makasudin zuwansa wannan yanki dake kasa da kilomita 20 da iyakar Mali.

Ya ce "nauyi ne da ya rataya a wuyana a irin wannan lokaci na zaman makoki inzo da kaina in gwada alhini sakamakon mawuyacin halin da kuke ciki. Kun yi asarar mutane 69 akasarinsu matasan kauyukan gundumar Banibangou. Nijer kaf tayi bakin cikin mutuwar wadanan mutane."

Sannan ya ci gaba da cewa "Nazo in kawo maku goyon baya amma kuma nazo in saurari bukatunku kuma naji bayanan ku nazo da dukan shugabanin jami’an tsaro cikinsu har da shugaban rundunar mayakan kasa domin su ma su saurari abubuwan da zaku fada su ji abubuwan da kuke bukata kuma su ji shawarwarin da zaku bayar".

"Ina so in sanar da ku cewa daga dukan damuyoyin da ke gabanmu matsalar tsaron da ake fama da ita a yankin Tilabery ita ce ke hana ni barci kuma hankalina ya fi karkata akanta fiye da komai".

Mohamed Bazoum ya lashi takobin murkushe matsalar tsaron da ta addabi wannan yanki.

Ya na mai cewa kalubale ne dake gaban kasarmu shine kalubalen farko da ke gabana a matsayina na shugaban kasa domin ni ya kamata a baku tsaro. Zan tunkari wannan kalubale da hadin kan daukacin asakarawan kasarmu da goyon bayanku.

A tsawon shekarun nan 10 mun lilika yawan sojojinmu sau 3 yawan jandarmomi kusan sau 2 haka jami’an garde Nationale da ‘yan sanda to amma da alama abin bai isa saboda haka zamu kara daukan Karin jami’an tsaro haka kuma zamu samarda Karin kayan aikin tsaro.

Shugaban kasa ya kudiri aniyar bullo da wani fasalin musamman domin tallafawa jama’ar karkarar Banibangou da ta Zarmanganda inda ake cikin matsanancin yanayin karancin abinci sanadiyar hare haren ta’addancin da suka hanawa ayyukan noma a damanar da ta gabata.

Bayanai sun yi nuni da cewa mutanen nan 69 da suka rasu a farkon makon jiya a Banigandou ‘yan aikin sa kai ne dake sintiri ba tare da izinin mahukunta ba saboda haka Mohamed Bazoum ya ankarar da al’umma cewa hukuma ce ke da hurumi da alhakin gudanar da aiyukan tsaro a ko ina a nan Nijer aikin da doka ta hannuntawa jami’an tsaro.

Saurari cikakken rahoton a cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:41 0:00


TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG