Shugaban Najeriya ya jagoranci sauran kasashen dake kewayen tafkin chadi a taron farfado da tafkin da ya kawo karshe a Abuja.
Shugaban Najeriya ya bukaci a tabbatar a wannan karon za'a shirya tsarin farfado da tafkin dalla dalla ba maganar ta sha ruwa ba bayan an kammala taron. Ya jaddada mahimmancin tafkin wanda kasashen Afirka ta yamma da ta Afirka ta Tsakiya suka dade su cin gajiyarsa.
Ya tuna masu yadda bushewar tafkin ya kawo matsaloli na zamantakewa da sufuri da ayyukan bunkasa tattalin arzikin yankin, musamman noma da cinikayya.
Shugaban Najeriya ya kira sauran takwarorinsa da kungiyoyi da babban bankin duniya da bankin Islama da kungiyoyin dake kula da rayuwar al'umma su himmatu wurin tabbatar da cewa an dauki matakan da suka kamata domin farfado da tafkin.
A cewar shugaban a karshen taron za'a fitar da matsayi na Abuja akan taron, wato za'a fitar da wata tausiya ce za'a yi anfani da ita wajen shirya jaddawalin aikin gyara tafkin dalla dalla. Ya ce duk masu ruwa da tsaki su amince da kudurin su tashi su yi aiki tukuru ba wai su mayar da taron wani taron shan shayi ba.
A saurari rahoton Umar Faruk Musa da karin bayani.
Facebook Forum