Shi dai ,wannan horo na ko cikin matakan da hukumar samar da aikin yi ta NDE,ke dauka a yanzu,don horas da 'yan gudun hijiran da rikicin Boko Haram ya shafa,inda sama da yan gudun hijira dubu biyu da dari biyar suka ci gajiyar shirin a Adamawa,daya daga cikin jihohin da balahirar Boko Haram ta fi shafa a Najeriya.
Yayin kaddamar da shirin,a sansanin 'yan gudun hijira dake Malkohi,kakakin majalisar dokokin jihar Kabiru Mijinyawa,ya ce tuni su a majalisar suka samar da doka domin kyautatawa wadanda tashe tashen hankulan Boko Haram suka shafa.
Mr Keneth Maigida shi ne shugaban riko na hukumar ta NDE a jihar Adamawa,ya yi karin haske game da wannan shiri na horas da 'yan gudun hijiran.
Shima Mr Midala Iliya,jami’in hukumar ba da agajin gaggawa, NEMA, a sansanin ya ce suna murna da wannan shiri na hukumar NDE.
Ahmad Abba Sudi da Shehu Muhammad Dankolo,da suka yi jawabi a taron sun shawarci yan gudun hijiran ne da su maida hankali wajen koyon sana’o’in domin kyautata rayuwarsu.
A saurari rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani.
Facebook Forum