Yayinda yake bude taron akan farfado da tafkin Chadi na kasa da kasa na kwanaki uku, da a ke yi a Abuja,, mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo, ya bayyana yadda tafkin ke bushewa zuwa kusan kashi casa'in cikin dari.
Mataimakin shugaban kasan ya ce bushewar da tafkin ke ci gaba da yi babbar matsala ce ga kasashen da suka dogara a kanshi.
Babban sakataren hukumar rayar da tafkin Injiniya Sanusi Imrana Abdullahi ya tabo halin da kasashen yankin tafkin Chadin ke ciki yanzu. Ya ce a yau kasashen yankin ke kan gaba wajen tabarbarewar ayyukan jinkai, lamarin da ya shafi mutane fiye da miliyan bakwai wadanda kungiyar Boko Haram ta raba da gidajensu. Akwai wasu miliyan biyu da sun dogara ne kacokan akan tallafi.Inji Injiniya Abdullahi yankin ne ke kan gaba wajen talauci baicin yawan haihuwa da rashin ilimi.
Tafkin ya ratsa kasashen Najeriya, Chadi, Nijar, Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, Algeria, Sudan, Kamaru da Libya.Masana na cewa raguwar ruwan tafkin ya zama masu bala'i.
A cewar Dan Masanin Fika Alhaji Bababa Abba tsohon sakataren hukumar raya kogin Kwara mai kasashen Afirka bakwai da kuma yake da alaka da tafkin Chadi ya ce wannan taron ya zo kan gaba. Ya ce an dade ana kokarin jawo hankalin kasashen da zasu iya taimaka saboda matasalar ta fi karfin kasashen da alamarin ya shafa. Ya yi misali da mutanen yankin arewa maso gabashin Najeriya wadanda ya ce babu wani albishir da za'a yi masu da zai wuce sake farfado da tafkin idan aka yi la'akari da ukubar da suka sha a hannun kungiyar Boko Haram. A cewarsa shekaru 20 da suka gabata ana iya tafiya mai nisa cikin jirgin ruwa akan tafkin amma yanzu ba haka lamarin yake ba.
A saurari rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani.
Facebook Forum