A wata sanarwa da hukumar ta NAFDAC ta fitar ta hannun kakakinta Abubakar Jimoh, ta ce hukumar ta dauki matakin kama kwalaben magungunan tari masu dauke da sinadarin Codeine ne bisa dokar hana sayar dashi a bainar jama’a ba bisa ka’ida ba da gwamnati ta dauka a kwanakin baya.
Darakta a hukumar NAFDAC Dakta Musa Umar, ya ce hukumar na kokarin ganin ta tabbatar da dokar cewa sai mutum yana da izini daga gurin likita kafin a sayar masa da duk maganin tari mai dauke da sinadarin Codeine. Matsalar kuma da ake fuskanta itace ba a bin wannan doka kamar yadda ya kamata.
Tuni dai hukumar ta NAFDAC ta kafa wani kwamiti da zai taimaka wajen magance wannan matsalar, kwamitin dai ya kunshi masana magunguna da likitoci.
Likitan hada magunguna Peter Iliya, ya bada shawarar cewa dole ne sai an hada karfi da karfe tsakanin gwamnati da jami’an tsaro da kuma jami’an lafiya, domin samun nasarar ganin an daina sayar da magunguna ba bisa ka’ida ba.
Abin jira a gani shine ko wanne mataki gwamnati za ta dauka wajen hukunta masu sha ko sayar da wadannan haramtattun magunguna.
Domin karin bayani saurari rahotan Babangida Jibrin.
Facebook Forum