Laraba majalisar zartaswar Nigeria ta amince da kudurori da bukatun da ma’aikatar shari’a ta gabatar mata dangane da bada goyon bayan da ake bukata wurin cika sharudan kungiyar Edmond Group.
Akwai kudurorin da ya kamata Nigeria ta aiwatar domin ta shiga jerin kasashen duniya dake cin moriyar kungiyar Edmond Group din, kungiyar dake taimakawa da bayanan sirri kan lamuran cin hanci da rashawa da wasu ayyukan asha kamar ta’addanci da safarar miyagun kwayoyi da makamai.
Ministan shari’a Abubakar Malami yace amincewar ta ba Nigeria damar shiga jerin kasashen dake muamala da wannan kungiyar kasa da kasa mai yaki da cin hanci da rashawa.
Abubakar Malami yace yanzu kasar zata yi aiki na bai daya da kungiyar domin a yaki cin hanci da rashawa gadan gadan. Y ace an samu daidaituwa akan abun da ya kamata a yi domin yaki da masu ta’ammali da kwayoyi da karkata kudade zuwa wasu wurare da kuma masu safarar muggan makamai da dai sauransu.
Akan jinkirin da gwamnatin Nigeria ta yi wajen amincewa ta yi aiki kafada da kafada da kungiyar Edmond Group har ta yi barazanar korar kasar, Abubakar Malami ya dorawa majalisar dokokin kasar alhakin jinkirin. Yace dole ne gwamnati ta jira amincewar majalisa kafin ta dauki mataki.
A saurari rahoton Umar Faruk Musa domin jin karin bayani
Facebook Forum