Janaral Dambazau yana amsa tambayoyin manema labaru ne yayin da ya fadi hakan a wani wurin taron tsarin tsarkake tsaro a Kaduna. Ya kara da cewa idan ana son magance matsalar tsaro akwai bukatar a dubi yanayin da arewa maso gabashin Najeriya ke ciki.
Janaral Dambazau yace harakar tsaro a arewa maso gabas ba harka ba ce da za'a barwa Najeriya ita kadai. A da shekaru hudu ko biyar da suka wuce ana iya bar ma kasar amma ba yanzu ba.
Harkar tsaro yanzu ta hadu da abubuwa dake fitowa daga kasashen Chadi, Kamaru, Niger da Mali da ma sauran wasu kasashe. Kada a manta makaman da ake anfani dasu ba a kasar a ke yinsu ba. Ana shigo dasu ne daga wasu kasashe. Najeriya ba zata iya hanasu shigowa ba sai an hada da kasashe dake makwaftaka da ita.
Janaral Dambazau yaci gaba da cewa ya kamata a dubi yanayin arewa maso gabas. Akwai matsalar hamada saboda haka babu maganar noma. Akwai rashin aikin yi. Akwai matsalar makaranta da ta bokon da ta islamiyar. Akwai kuma matsalar talauci. Babu aikin yi kuma babu kudi, babu abinci. Duk wanda yake son yayi anfani da mutumin dake cikin yunwa to zai yi anfani dashi domin ya cimma burinsa. Sabili da haka ba karfin soja ba ne kawai za'a yi anfani dashi. A dubi wannan fuskar, idan kuma ana neman gyara za'a gyara.
Shi kuwa Farfasa Saddiq Zubairu Abubakar na jami'ar Ahmadu Bello Zaria, cewa yayi idan ana son a magance matsalar tsaro a Najeriya to sai a hako tushenta. Kada a kalli abun ta fuskar siyasa kawai domin ba za'a ci nasara ba. Sai an koma ta fuskar anfani da arzikin da Allah yayi ma kasar na ruwa da kasa. Sai an koma an gyara kuren da aka yi. Sai an yi zama na musamman da masunta da makiyaya da manoma an yi yarjejeniya, an yi tsare-tsare kowa a bashi hakinsa. Kowa nada bukatan abun kuma su ne suke habbaka tattalin arzikin kasar gaba. A cikin duk tsarin harkar tsaro da za'a yi sai a hararo wadannan a kuma ba batun mihimmin gurbi a tattaunawar da za'a yi.
Amma wani mazaunin kudancin jihar Kaduna da ya san harkar tsaro a yankin Malam Bala Adamu Kafanchan yace yana da ra'ayi daban. Yace abun da zai kawo fahimtar juna da karewar matsalar tsaro shi ne duk sarakuna, shugabannin al'umma, masu fada a ji, shugabannin addinai na yankin a zauna gaba daya a tattauna ido da ido idan ba haka ba duk aikin banza ne.
Ga rahoton Isa Lawal Ikara.