An karyata rahotanni da aka bayar tunda farko cewa, an gano baraguzan jirgin kusa da wani tsibiri a kasar Girka. Hukumomi sun tabbatar da cewa zuwa yanzu dai basu gano wani abu na daga jikin jirgin ba.
Masar tace, da alamun ta'addanci ne dalilin da ya haddasa faduwar jirgin, maimakon wani lahani na daban, duk da haka babu takamammen bayanin abunda ya janyo hadarin jirgin zuwa yanzu.
Jirgin, kirar Airbus, dauke da mutane 66, kwatsam yayi kwana, kuma nan da nan ya fara subutowa, kamin ya bace daga na'urar hangen nesa da ake kira Rader da turanci. Lamarin ya auku ne da asubahin jiya Alhamis.
A Masar, ministan zirga zirgan jiragen sama Sherif Fathy, yace idan matsalar ta tsaro ce, to alhakin yana kan Faransa, muddin aka tabbatar cewa ta'addancin ne dalilin faduwar jirgin.
Shugaban Amurka Barack Obama ya sami karin bayani dangane da wannan lamari. Kakakin Fadar shugaban kasar, Josh Earnest, ya mika ta'aziyya kan hadarin, amma ya jaddada cewa kada a yi riga malam masallaci kan musabbabin faduwar jirgin tukuna.