Wannan shi ne karo na farko a tarihin kungiyar kwadago da aka janye zanga zangar yajin aiki ba tare da rage ko kwandala ba a farashin man fetur wanda yanzu yake nera 145 kowace lita daga nera 86.5.
Shugaban kungiyar Ayuba Wabba yace kungiyar tayi dogon nazari ne da rokon shugaban APC Bola Tinubu yayi yayainda ya yi tattaki zuwa hekwatarsu. Wabba yace idan basu saurari irin su Tinubu ba to wanene kuma zasu saurara. Tinubu ya rokesu da su bashi dama, idan sun janye yajin aikin, za'a koma teburin sasantawa.
Ma'ajin kungiyar kuma shugaban kungiyar ma'aikatan kananan hukumomin Najeriya Kwamred Ibrahim Khalil yace yana ganin ma'aikatan kasa basu hango abun da kungiyar ta hango ba. Yace dagewar da suka yi suka fito ba karamar nasara ba ce. Rarrabuwa da suka samu da tsoffin 'yan kwadago da yanzu suka zama 'yan siyasa tare da kasancewa cikin gwamnati sun yi masu zagon kasa amma duk da haka sun dage.
Mutane na cigaba da kira a kai zuciya nesa da rokon a ba gwamnatin Buhari lokaci wadda a wannan watan zata cika shekara daya kan mulki. Ahmad Muhammad Gombe wani masanin tattalin arziki yace duk abun da ake gani cewa an shiga wani tsanani nan ba da jimawaba za'a samu saukinsa.
Ga karin bayani.