Shugaban Koriya Ta Arewa Kim Jong Un, ya kai ziyara China cikin makon nan, sai dai ziyarar bata aiki ba ce, kamar yadda kamfanin dillancin labaran kasar Xinhua ya bada rahoto akai yau Laraba.
Wannan ziyarar itace ta farko, ga shugaban wanda saniyar ware ne, tunda ya kama aiki a shekara ta 2011.
Rahotanni a kafofin yada labarai sun ce wani jirgin kasa da aka hakikance yana dauke da wata tawaga daga Koriya ta Arewa ta bar Beijing akarkashin wani matakin tsaro mai tsanani a birnin. Sai dai babu tabbas kan wanda ke cikin jirgin.
Masu fashin baki suka ce ziyarar tana iya zama wata babbar mataki na sauya alkiblar kasar daga fito na fito ta koma amfani da difilomasiyya.
Facebook Forum