Shugabannin Koriya ta Arewa da na Kudu, Kim Jong Un da Moon Jae-in sun hadu a gari mai tarihi, Panmunjom, inda a nan ne kasashen biyu suka taba cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a bayan yaki tsakaninsu a shekarar 1953, domin fara zaman tattaunawa tsakaninsu. Wannan shine karo na uku da aka taba gudanar da taron koli tsakanin kasashen biyu amma wannan shine karo na farko da aka samu wani shugaban na Koriya ta Arewa da ya kaiwa makwabtarsu ta kudu ziyara.
A karon farko Shugaban Koriya Ta Arewa Ya Ketara Zuwa Koriya ta Kudu

1
Shugaba Kim Jong Un tare da dogarawansa a lokacin da ya iso taron a garin Panmunjom ta bangaren kasarsa.

2
Shugaban Koriya Ta Arewa tare da takwaransa na Koriya ta Kudu a lokacin da suka isa iyakar kasashen biyu a garin Panmunjom.

3
A karon farko Shugaban Koriya Ta Arewa Ya Ketara Zuwa Koriya ta Kudu

4
Shugaban Koriya Ta Arewa da takwaransa na Koriya ta Kudu yayin da suke tafiya cikin kauyen Pamunjom.