An rantsar da tsohon daraktan hukumar leken asirin Amurka Mike Pompeo a matsayin sakataren ma'aikatar harkokin wajen Amurka jiya Alhamis, bayan 'yan majalisar dattawa 42 a cikin 54 suka tabbatar da mutumin da Shugaba Donald Trump ya zaba, da dukan yan jam'iyar Republican suka goyi baya, duka 'yan jam'iyar Democrat kuma banda mutum shida 6, da kuma wani dan Independa guda daya suka kada kuri'ar rashin goyon bayansa.
Pompeo ne ya maye gurbin Rex Tillerson wanda Trump ya kora watan da ya gabata, zai fara aiki da halartar wani taron kungiyar tsaron hadin guiwa ta NATO a Brussels a ranar juma'a inda zai tattauna da ministocin harkokin kasar wajen Turkiyya da Italiya.
Sabon sakataren ma'aikatar harkokin wajen Amurkan daga nan zai wuce kasashen Isra'ila, Saudiya, da kuma Jordan. Mai Magana da yawon ma'aikatar harkokin wajen Amurka Heather Nauert tace an zabi wuraren da zai yada zango ne, a nuna irin muhimmancinsu a matsayin manyan abokan kawancen Amurka a yankin.
Ziyarar tazo ne jim kadan bayan an tabbatar dashi bayan zabe mai cike da hamayya a majalisar Dattijan Amurka inda yan majalisar Republican suke goyon bayan Pompeo, yawanci yan Democrats sun koka ne akan ganin dan takarar ya nuna kyama ga musulmai da yan masu neman jinsi daya.
Facebook Forum