Tuni ‘yan kasar suka fara tofa albarkacin bakinsu akan yadda suke kallon abinda suke kira sabuwar tafiyar al’amuran mulki.
Sakataren gwamnatin jamhuriyar Nijer Abdou Dan Galadima ya gabatar da wata sanarwa mai dauke da sunayen ministocin gwamnatin fira minista Ouhoumoudou Mahamadou mai mambobi 33 maza da mata abinda ake ganinsa a matsayin wani matakin share fagen shinfida sauyi a wannan kasa idan aka yi la’akari da gwamnatin da ta shude mai ministoci sama da 40.
A cewar wani mai kare muradun jam’iyar PNDS Tarayya Mohamed Abdoulkader matakin takaita yawan ministoci a sabuwar gwamnatin alama ce ta soma cika alkawulan da Bazoum Mohamed ya dauka a jawabin bukin rantsar da shi a ranar juma’ar da ta gabata.
Koda yake ya yaba da matakin shigar da matasa a sabuwar gwamnatin jami’in fafitika Abdou Alhaji Idi na cewa akwai alamar an yi kitso da keya saboda nadin wasu ministoci a kalla 10 daga cikin wadandasuka kaurin suna agwamnatin da ta shude.
Haka dai shi ma Alhaji Salissou Amadou na kungiyar Sauvons le Niger ke ciza yatsa saboda fargaba a game da koma bayan da za a yi fuskanta wajen yaki da mahandama dukiyar kasa a bisa la’akari da wasu ministocin sabuwar gwamnatin.
Daga cikin ministoci 33 jam’iyar PNDS Tarayya madugar kawanccen jam’iyun dake mulki na da kujeru 16 cikinsu har da ta ministan tsaro da ta ministan cikin gida da ta ministan kudin kasa da ta man fetur yayinda MPR jamhuriya ke da ministoci 5 MNSD Nassara 4 sai CPR Inganci kujeru 3 sannan sauran kananan jam’iyu ke da kujera guda guda..
Kimanin mata 6 ne ke gwamnatin ta Ouhoumoudou Mahamadou yayinda a karon farko wani matashi Ahmat Djidoud ke rike da ma’aikatar kudi ta kasa sai Maman Sani Issouhou Mahamadou da aka baiwa mukamin ministan man fetur da makamashi.
Saurare cikakken rahoton Souley Barma a sauti: