Rahotanni daga Jamhuriyar Nijar na cewa, kura ta lafa bayan da aka kwashe kusan minti 30 ana jin karar harbe-harbe a yankin fadar shugaban kasar da ke birnin Yamai.
Da sanyin safiyar ranar Laraba aka ji harbe-harben bindiga, inda rahotanni suka ce an kwashe kusan minti 30 ana jin karar.
Karin bayani akan: Mahamadou Issoufou, Shugaba Muhammadu Buhari, Mohamed Bazoum, Mahamane Ousmane, Jamhuriyar Nijar, PNDS, Nigeria, da Najeriya.
Wakilin Muryar Amurka a Yamai, Souley Moumouni Barma, ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya ce abin ya faru ne da misalin karfe uku na tsakar dare.
Rahotanni sun ce an kama wasu daga cikin sojojin da suka yi yunkurin juyin mulkin, yayin da shugabansu ya tsere.
Bayanai sun ce wasu sojojin sama ne cikin motoci guda biyar suka far wa fadar shugaban kasar, amma hakarsu ba ta cimma ruwa ba.
Ko da yake har yanzu, hukumomin kasar ba su ce uffan kan wannan lamari ba, amma bayanai na nuni da cewa an kashe wasu daga sojojin da suka yi kokarin kifar da gwamnatin shugaba Issoufou, wanda ya rage mai kwana biyu ya sauka a mulki.
Da ma dai ana zaman dar-dar a kasar ta Nijar, wacce ke yammacin Afirka, tun bayan zaben shugaban kasar da aka yi a ranar 21 ga watan Fabrairu a zagaye na biyu, wanda jam’iyya mai mulki ta PNDS ta lashe.
Wannan al’amari na faruwa ne kwana biyu gabanin a mika mulki ga zababben shugaban kasa Mohamed Bazoum wanda zai gaji shugaba Issoufou Mahamadou mai barin gado.
Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto gwamnati ba ta ce komai game da abin da ya faru.
Amma wasu kafofin yada labaran kasar na yanar gizo sun ruwaito cewa yunkuri aka yi na juyin mulki.
A makon da ya gabata, kotun tsarin mulkin kasar ta ayyana Bazoum, mai shekara 61, a matsayin wanda ya lashe zaben.
Sai dai dan takarar bangaren adawa Mahamane Ousmane na jam’iyyar RDR na kulabantar sakamakon zaben, inda ya ce an tafka magudi.
A ranar Litinin, Ousmane, mai shekara 71, wanda tsohon shugaban kasa ne, ya yi kira ga magoya bayansa da su shirya yin zanga-zangar lumana.
Bazoum, tsohon ministan cikin gida ne, kuma na hannun daman shugaba Issoufou.
Nijar dai kasa ce da ta sha fama da juyin mulki, inda na karshe da ta gani shi ne na 2010, a lokacin da sojoji suka kifar da gwamnatin marigayi tsohon shugaba Tandja Mamadou.
Amurka Ta Rufe Ofishin Jakadancinta
A halin da ake ciki, ofishin jakadancin Amurka da ke Yamai, ya yi kira ga ma’aikatansa da su zauna a gida bayan aukuwar harbe-harben.
“Ofishin jakadancin Amurka zai kasance a rufe a ranar 31 ga watan Maris, 2021 saboda harbe-harben bindiga da aka ji a kusa da unguwarmu.” Wata sanarwa da ofishin ya wallafa a shafin yanar gizonsa ta ce.
Ofishin jakadancin Amurka, ba shi da nisa sosai da fadar shugaban kasar ta Nijar.
“Muna masu kwadaitar da dukkan ma’aikata da su zauna a gida har sai yadda hali ya yi.”
Sanarwar ta kara da cewa, akwai yiwuwar barkewar rikici a sassan kasar “a wannan lokaci na bayan zabe.”
Yadda Gwamnatin Nijar Ta Dakile Yunkurin Juyin Mulki