An kammala wani taro a fadar shugaban kasar Nijar Issouhou Mahamadou wanda ya tattara manyan hafsoshin soja da jakadun Amurka da Faransa, mako guda, bayan mummunan harin da ya hallaka sojojin Nijar a wani kauyen Tilabery mai iyaka da kasar Mali.
Taron, wanda shi ne makamancinsa na farko da ke hada hukumomin tsaron Nijar a daya gefen kuma da kasashen Amurka da Faransa, na matsayin wani matakin nazarin hanyoyin zartar da shawarwarin da aka tsayar a tantaunawar da ta hada Shugaba Issouhou Mahamadou ta wayar tarho da Shugaba Donald Trump da Shugaba Emmanuel Macron da nufin sake karfafa matakan yaki da ‘yan ta’adda. Alhaji Kalla Moutari shine Ministan Tsaron kasar Nijar.
Hada karfi domin kaddamar da farmakin hadin guiwa a fagen fama tsakanin sojojin Nijer da takwarorinsu na Amurka da Faransa na daga cikin sabbin dubarun da ake saran zartar da su a nan gaba domin kakkabe masu tayar da kayar baya a wannan yanki.
Jakadan Amurka a Nijar Amb Eric P. Whitaker ya jaddada cewa gwamnatin Amurka za ta ci gaba da tallafawa wannan kasa a dukkan fannonin da aka saba diflomasiyya da ayyukan ci gaban kasa da tsaro.
Sannan ya kara da cewa tsaro da kwanciyar hankali wasu abubuwa ne da sai da su ake samun sukunin bayarda kowane irin tallafi, sabili kenan da ya sa za mu ci gaba da bai wa jami’an tsaron Nijar horo da kayan aiki, don ganin sun samu kwarin gwiwar tunkarar barazanar tsaron da ake fuskanta a yau.
Jamhuriyar Nijar ta fuskanci hare haren ta’addanci da dama a makon jiya, a yankin Tilabery. Mafi muni shi ne wanda ya yi sanadin mutuwar sojojinta 29, wadanda ‘yan bindiga suka yi wa kwanton bauna a dai-dai lokacin da wata motarsu ta taka nakiya a kauyen Balley Beri kusa da Tongo Tongo mai iyaka da Mali.
Saurari cikakken rahoton wakilin Muryar Amurka: Souley Moumouni Barma
Facebook Forum