A jiya Laraba, shugaban kamfanin kera motar Volkswagen Martin Winterkorn ya ajiye aikinsa, a daidai lokacin da ake kan badakalar kamfanin Jamusawan.
Game da yadda kamfanin ya yi kumbiya-kumbiyar kaucewa kula da yawan motocin da zasu kera har guda Miliyan 11, don kaucewa gwajin gurbatar yanayi.
Winterkorn yace, ya dauki alhakin laifin matsalolin da aka gano a injin motocin, amma yace bashi da masaniya game da wani aikata ba daidai ba. Yace kamfanin na bukatar sabon yanayin fara aiki da kuma ma’aikata.
A cewarsa, murabus dinsa zai bada wannan dama. Ya yi kira ga kamfanin da su ci gaba da aiwatar da tsarin aiki a bisa tantancewa kuma a bayyane.