Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Jamhuriyyar Nijar Ya Sami Lambar Yabo Ta MO Ibrahim


Shugaba Issouhou Mahamadou
Shugaba Issouhou Mahamadou

Gidauniyar kasar Birtaniya ta MO Ibrahim mai burin kawar da mulkin kama karya a kasashen Afirka ta karrama shugaban kasar Jamhuriyyar Nijar Issouhou Mahamadou da lambar yabo.

Gidauniyar ta karrama shugaban kasar ne saboda abin da ta kira nasarorin da ya samu wajen kyautata dimokaradiyya da samar da ci gaban al’umma a tsawon shekaru 10 da ya yi a kan karagar mulki.

Taron kwamitin shugabannin Gidauniyar ta MO Ibrahim ne ya yanke shawarar baiwa shugaba Issouhou Mahamadou lambar yabo sakamakon gamsuwa da kamun ludayinsa a tsawon shekarun da ya yi a kan karagar mulki.

Mo Ibrahim, wanda ya kafa gidauniyar Mo Ibrahim Foundation
Mo Ibrahim, wanda ya kafa gidauniyar Mo Ibrahim Foundation

kwamitin ya bayyana cewa, shugaban ya cika akasarin mahimman sharudan da aka gindaya kafin samun wannan matsayi.

A hirar shi da Muryar Amurka, Alhaji Ouhoumoudou Mahamadou wanda ya shafe shekaru 9 yana jagorancin fadar shugaba Issouhou, ya ce wannan abin murna ne ace dan Nijar ya samu wannan lambar yabo wanda ta ke da wahalar samu.

Ya kuma kara da cewa, Mahamadou Issouhou ya cika dukkan ka’idojin da ake bukata na mika mulki ba tare da gardama ba da ayyukan da ya yiwa kasa da kuma nunawa jama’ar duniya yana girmama dokokin kasa.

Shugaban Jamhuriyar Nijar, Issoufou Mahamadou
Shugaban Jamhuriyar Nijar, Issoufou Mahamadou

Shekaru 4 ke nan gidauniyar Mo Ibrahim da ke gudanar da bincike domin tantance shugaban kasar da ya cancanci samun wannan lambar yabo ta yunkurin kawar da mulkin kama karya a kasashe masu tasowa ba ta sami wanda ya cancanci samun wannan lambar yabon ba.

Shugaba Issouhou Mahamadou wanda zai sauka daga kujerar mulki a ranar 2 ga watan Afrilun mai zuwa shine shugaban kasa na 6 da ya taba samun wannan tukwici da ke kunshe da dalar Amurka miliyan 5 wadanda za a biya cikin tsawon shekaru 10 .

Da yake bayyana matsayinsa a shafinsa na Tuwita shugaban ya sadaukar da wannan tukwici ga al’ummar Nijar kuma a cewarsa abu ne da ke kara masa kwarin gwiwar ci gaba da ayyukan karfafa dimokradiyya a wannan kasa da ma kasashen Afirka baki daya.

Saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:42 0:00


XS
SM
MD
LG