Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Iran Ya Yabawa Dokar Yaki Da ‘Yan Luwadi a Uganda


Shugaban kasar Iran Ebrahim Raisi tare da shugaban kasar Uganda's President Yoweri Museveni.
Shugaban kasar Iran Ebrahim Raisi tare da shugaban kasar Uganda's President Yoweri Museveni.

Shugaban kasar Iran Ibrahim Raisi ya kai ziyara kasar Zimbabwe jiya Alhamis, inda ya kammala ziyarar kasashen Afirka uku da ya kai Kenya da Uganda.

Yayin da yake kasar Uganda, Raisi ya ce kasashen Yamma suna tallata luwadi da madigo domin kawo karshen abin da ya kira “makomar zuri’ar dan Adam”.

Ziyarar ta Raisi ta zo ne bayan a watan Mayun da ya gabata Uganda ta rattaba hannu kan wata doka mai tsauraran hukunce-hukunce kan ‘yan luwadi da madigo ciki har da hukuncin kisa.

Wasu maza 'yan luwadi da aka kama
Wasu maza 'yan luwadi da aka kama

A lokacin ziyararsa ta yini guda a Uganda a wannan makon, Raisi, wanda ke magana ta bakin tafinta, ya bayyana luwadi da madigo a matsayin wani hari da ke adawa da tubalin gina zuri’a da gado, fanin da a cewarsa, Uganda da Iran za su iya yin hadin gwiwa.

Shuwagabanin kasashen Iran da Uganda
Shuwagabanin kasashen Iran da Uganda

"Kasashen Yamma suna ƙoƙarin maida luwadi a matsayin alamar wayewa, yayin da wannan yana ɗaya daga cikin batutuwa mafi ƙazanta," in ji shi.

Raisi ya yi wannan tsokaci ne domin nuna goyon bayansa ga matakin da Uganda ta dauka na abin da aka bayyana a matsayin daya daga cikin dokoki mafi tsauri a duniya kan 'yan luwadi.

Masu goyon bayan 'yan luwadi a Uganda
Masu goyon bayan 'yan luwadi a Uganda

Dokar, wacce aka zartar a watan Mayu, ta sanya hukuncin kisa kan masu aikata luwadi da kuma hukuncin daurin shekaru 20 a gidan yari saboda tallata aikin. Matakin ya sa wasu 'yan kasar Uganda tserewa zuwa makwabciyar kasar Kenya.

Shugaban Amurka Joe Biden ya bayyana matakin a matsayin "bai dace ba" da kuma "abin kunya ne."

Wani mai fafutukar kare hakkin bil adama Frank Mugisha ya ce: "Suna ci gaba da cewa kasashen Yamma suna tura akidunsu kan Uganda, amma duk da haka muna da wasu kasashe masu tsoma baki tare da ingiza nasu kimar a Uganda," in ji shi. "Alal misali, Iran - mun san suna goyon bayan kungiyoyi masu adawa da luwadi a nan kasar."

Mugisha ya ce tun lokacin da aka kafa dokar haramta luwadi, ‘yan luwadi sun fuskanci cin zarafi da dama daga masu ba da hayar gidaje da kananan hukumomi.

Ziyarar da Raisi ya yi a wasu kasashe uku na Afirka wani yunkuri ne na bunkasa alakar diflomasiyya ta Iran da nahiyar.

Dandalin Mu Tattauna

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG