Majalisar dokokin Jamhuriyar Nijar ta bayyana shirin yin wani zama na musamman a nan gaba, domin nazari a kan kudirin dokar da gungun wasu ‘yan majalisar ya gabatar da nufin kafa dokar hukunta ‘yan madigo da masu luwadi.
Wanna na zuwa ne bayan la’akari da barazanar lalacewar tarbiyar da ake fuskanta a wannan lokaci da kafafen sada zumunta ke zama wani bangare na rayuwar al’ummar kasar.
Tun a watan Oktoban da ya gabata ne, gungun wasu ‘yan majalisar dokokin kasa ya shiga yunkurin ganar da daukacin ’yan majalisar a kan bukatar kafa dokar hukunta masu aikata dabi’un da ke barazanar gurbata tarbiya.
Sakamakon lura da abin da suka kira sabon yayin da matasa masu amfani da kafafen sada zumunta suka bullo da shi musamman inda yada bidiyo da hotunan batsa ke kokarin zama ruwan dare.
Mai magana da yawun wadanan ‘yan majalisa, Honorabul Nana Djoubie Harouna, ta ce rufe ido a kan wannan bakon al’amari tamkar dama ce aka bai wa masu luwadi da ‘yan madigo su baje koli a wannan kasa.
Wannan ya sa a wannan ranar Alhamis 8 ga watan Disamba suka gabatar da wani kudirin dokar a ofishin kakakin majalisar, don ganin an bi hanyoyin tafka mahawara a kansa a nan gaba kadan.
‘Yan majalisar sun ce suna da kwarin gwiwar samun hadin kan dukkan bangarori a abinda suka kira gwagwarmayar kare al’ummar Nijar da al’adunsu.
‘Yar majalisar dokokin kasa, Honarabul Ousseina Madougou, ta yi kira ga duka mata da hada hannu don shawo kan wannan lamari, tun da abun su ya shafa kuma wadannan ‘ya’yansu ne wannan abun akwai ciwo, domin mutane hankalinsu ya kwanta.
Farfado da wannan magana ta kafa dokar hukunta masu luwadi da ‘yan madigo a Nijer wani abu ne da ke zuwa a wani lokacin da jama’ar kasar ke tafka mahawwara a kafafen sada zumunta dangane da wata sanarwar da aka wallafa a matsayin gayyata zuwa wurin wani gangamin goyon bayan ‘yan madigo da masu luwadi da ake saran gudanarwa a birnin Yamai a ranar 24 ga watan disamba.
Saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma: