Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya – EFCC, Abdulrasheed Bawa ya ce yana samun sakonnin da ke barazana ga rayuwarsa daga wasu manyan ‘yan Najeriya, a yayin da ya tamke damarar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasar zagon kasa.
Yayin da yake bayani a gidan talabijin na Channels, Bawa ya ce ko a makon jiya yana a birnin New York na kasar Amurka, wani babban mutum ya karbi kiran wayar tarho daga wani wanda ba ya ma ciki komar binciken hukumar, yana cewa za su kashe shugaban hukumar EFCC.
Karin bayani akan: EFCC, Abdulrasheed Bawa, Amurka, Nigeria, da Najeriya.
Ya ci gaba da cewa ko baya ga wannan ma, ya yi ta samun sakwannin da ake yin barazana ga rayuwar sa daga wasu manyan ‘yan Najeriya da hukumar ke bincike akan su.
Bawa ya ce yanayin yadda yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya ya ke mai da martani ya yi munin gaske.
Sai dai duk da haka ya ce sam wadannan barazanar ba za su tsorata su ba, inda ya lashi takobin cewa hukumar za ta ci gaba da tsayuwa kaimun waje tabbatar da kawar da ayyukan cin hanci da rashawa a kasar.
Shugaban na EFCC ya yi korafin cewa cin hanci da rashawa ya yi katutu a zukatan ‘yan Najeriya a ko ina, amma ya ce yana da yakinin cewa za su yi nasara a fafutukar da suke yi na kawar da mummunar dabi’ar a Najeriya.
Ya ce hukumar na nan tana kokarin kaddamar da hadin gwiwa da shugannin addinin Musulunci da na Kirista wajen fadakar da al’umma akan munin ayukan cin hanci da rashawa, sakamakon tasirin da addinai suke da shi ga ‘yan Najeriya.
Sabon Shugaban Hukumar EFCC Ta Najeriya Bai Ba Da Kunya Ba