Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban China Xi Jinping Ya Kai Ziyarar Farko A Birnin Wuhan


Chinese President Xi Jinping Coronavirus
Chinese President Xi Jinping Coronavirus

Shugaban China Xi Jinping ya kai ziyarar farko a birnin Wuhan a yau Talata, tun lokacin da cutar coronavirus ta barke a yankin, wacce ta kama sama da mutane dubu tamanin kana ta hallaka wasu dubu da dari daya a China.

Ma’iakatar yada labaran gwamnatin China ta ce, Xi zai ziyarci ma’aikatan kiwon lafiya da marasa lafiya tare da binciken kokarin da ake yi na dakile barkewar cutar.

Ziyarar na zuwa ne a lokacin da jami’an lafiya suka ce an samu sababbin wadanda suka kamu 19 a yau Talata, lamarin dake nuna ana ci gaba da samun raguwar yaduwar cutar a China, yayin da cutar ke kara yaduwa cikin gaggawa a wasu kasashe. An riga an shawo kan kimanin kashi 70 cikin dari na cutar a China.

A cikin matakan da ta dauka, China ta rufe manyan wurare domin dakile yaduwar cutar a manyan tarukan jama’a ko kuma tsakanin matafiya da zasu tafi wasu wurare a cikin kasar.

Kasar Italiya ita ma tana daukar irin wannan mataki bayan da ta zama daya daga ciki kasashen da cutar tayi tsananin bazuwa bayan kasar China, inda mutane sama da dubu tara suka kamu kana wasu dari hudu da sittin suka mutu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG