Shugaba Donald Trump na Amurka ya taya takwaran aikin na Rasha murnar nasarar da ya samu na sake zabensa. Mr. Trump ya mika masa sakon tayin murnar a wata tattaunawar da shugabannin biyu suka yi ta wayar tarho jiya Talata, har suka amince zasu gana a wani lokaci nan bada jumawa ba.
"Wata kila zamu gana nan bada jumawa ba, domin mu tattauna kan batun makamai, mu tattauna kan gasar tara makamai." Shugaban na Amurka ya gayawa manema labarai kamin ya gana da Yerima mai jiran gado na saudiyya Mohammed bin Salman.
Mr. Trump ya ce gasar kera makaman "yana so ya wuce makadi da rawa," amma Amurka, ba zata kyale wata kasa ta mallaki ko kusa da abunda Amurka ta mallaka ba." Cikin wasu batutuwa da shugabannin biyu zasu tattauna akan su sun hada da batun Ukraine, da Syria, da Koriya ta Arewa, inji shugaban na Amurka.
A tattaunawar da shugabannin biyu suka yi ta wayar tarho, shugaba Trump ya jaddada muhimmancin kawar da makaman Nukiliya a zirin Koriya.
Wata sanarwa daga fadar Kremlin, a jiya talata, ta ce,shugaba Trump, da Putin sun yi magana kan muhimmancin aiki tare a kasa-da kasa domin yaki da ta'addanci,takaita yaduwar makaman kare dangi, da kuma hada kai ta fuskar tattalin arziki.
Facebook Forum