Gwamnatin Amurka tabi sahun sauran kasashen duniya wurin yin ALLAH waddarai da harin da kasar takai da wani sinadari mai guba a Birtaniya ga wani tsohon mai leken asiri.
Haka kuma wannan ne karo na farko da Amurkan ta kakaba takunkunmi ga kassar ta Rasha akan zargin ta da aka yi mata game da kutse a harkokin zaben Amurka.
Da Manema labarai suka tambayi shugaba Donald Trump game da guban da aka sa ma wani tsohon mai liken asirin a Salisbury, sai yace ga bisa dukkan alamu kasar Rasha ce ta aikata wannan aika-aikan.
Kana ya bayyana wannan yunkurin kissan na wannan tsohon mai liken asirin a babban abin bakin ciki, yace Amurka ta dauki wannan batu da muhimmamci kamar yadda sauran kasashen duniya suka yi.
Sai dai da farko shugaba Trump yayi dari-dari wajen sukar shugaba Puttin ko kuma daukar mataki mai tsanani game da wannan batu.
Dafarko dai shugaba Trump ya fada ya nanata cewa ba ko wane alaka tsakanin tawagar kwamitin yakin neman zabensa da kasar ta Rasha, don haka binciken ma da Amurka keyi akan wannan zargin ba kome bane illa bita da kulli.
A jiya ne dai Amurka tabi sahun kasashe kamar su Birtaniya, Faransa Jamus na goya wa Birtaniyan baya akan cewa Rasha ke da alhakin kai harin sinadarin nan mai guba ga tsohonmai liken asiri.
Facebook Forum