Shugaban Amurka Barack Obama yace matsalolin da tattalin arzikin Rasha yake fuskanta ya nuna cewa shugaba Vladimir Putin bai kure shi ko Amurka ba.
A wata hira da yayi da tashar talabijin ta CNN jiya lahadi, Mr. Obama yayi watsi da ikirarin da ake yi cewa Mr. Putin "maradonna: ne, wanda ya kure Amurka da kasashen yammacin duniya, a gwagwarmayar da ake yi kan kasar Ukraine.
Mr. Obama yace, Mr. Putin yana fuskantar "rugujewar darajar kudin kasarsa, da kuma mummunan komadar tattalin arziki". Matsalar kudi da Rasha take fuskanta ya biyo bayan takunkumin karya tattalin arziki da Amurka da kuma tarayyar turai suka azawa kasar, bayan da hukumomin kasar da suke Moscow ta kama yankin Crimea a farkon wannan shekara.
Mr. Putin yana ci gaba da bijirewa, duk ana ganin kasar tana fuskantar gagarumin komadar tattalin arziki da faduwar farashin mai a kasuwannin duniya ya janyo, da kuma faduwar darajar kudin Rasha da ake kira Rubbles wanda yayi baya da kashi 40 cikin dari na karfinsa.
Mr. Putin yana gargadi kan 'yan kasar su shirya zasu shiga wani mawuyacin hali cikin kwanaki da watanni masu zuwa.
Yace kasarsa ba zata bada kai buri ya hau ba, daga ci gaba da goyon bayan 'yan Rasha a zirin Crimae. Ma'aikatar harkokin wajen kasar tayi alkawarin zata maida martani kan takunkumin da kasashen yammacin duniya suka azawa kasar.