A halin da ake ciki kuma, shugaba Rodrigo Duterte yace yana da niyyar tambayar Beijing a yayin taron kungiyar hadin kan tattalin arzikin kasashen yankin Asiya da Pacific da ake kira APEC a takaice, ko menene shirin kasar a kan tekun kudancin China, kuma ko za a kyale kasashen da suke kudu maso gabashin Asiya su yi zirga-zirga a tekun ba tare da tsangwama ba.
A cikin kusan watanni goma sha takwas da ya yi bisa karagar mulki, Duterte ya dauki salon lalama a dangantakarsa da Beijing da kuma batun ikirarinta na mallakar tekun kudancin China.
Kakakin shugaban kasar Ernesto Abella, ya bayyana a cikin watan Oktoba na shekara ta dubu biyu da goma sha shida cewa, sa’in-sa ba zai taimaki kasar Philippines ba, dalili ke nan da ya sa Duterte ya gwammace daukar matakin tattaunawar da zata tabbatar da kare mutuncin Manila.
Facebook Forum