Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Amurka Ya Jingine Barazanar da Ya Saba Yiwa Koriya ta Arewa


Shugaban Amurka Donald Trump da shugaban Koriya ta Kudu Moon Jae-In
Shugaban Amurka Donald Trump da shugaban Koriya ta Kudu Moon Jae-In

A jawabin da ya yiwa Majalisar Dokokin Kasar Koriya ta Kudu, a ci gaba da ziyararsa a nahiyar Asiya, shugaban Amurka ya yi sassauci da kalamunsa saboda bai caccaki Koriya ta Arewa ba kuma bai tozarta ta ba kamar yadda ya saba yi da can

Shugaba Donald Trump ya jingine barazanar da ya saba yi wa Korea ta Arewa, inda a jiya Talata ya gabatar da wani jawabin kara kwarin gwiwa ga Korea ta Kudu, yana mai cewa, “za a samu mafita” dangane da barazanar da hukumomin Pyongyang ke yi na makamin nukiliya.

Bayan kwashe yinin da ya yi yana wasu tararruka da bayyana a baina jama’a tare da shugaban Korea ta Kudu, Moon Jae-in a Birnin Seoul, shugaba Trump, ya ce an dauki matakan diplomasiyya wajen yayyafa ruwan sanyi kan takaddamar da ta dabaibaye yankin na Korea.

Wadannan kalamai na Trump sun sha banban matuka da sakonnin Twitter da ya rika wallafawa a ‘yan makwannin bayan nan, inda ya rika nanata cewa hawa teburin tattaunawa da hukumomin Pyongyan domin nemo bakin zaren takaddamar mallakar makamin nukiliyan, duk bata lokaci ne.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG