Kakakin fadar white House Josh Earnest ya fada jiya Alhamis cewa hakan ne yasa shugaba Obama yake sahun gaba na jaddada muhuimmancin zartas da doka wacce zata magance haka, da inganta tsaron kasa tareda tabbatar da an yi adalci ga kowa.
Wannan martanin ya biyo bayan wasikar da wakilan majalisar dokokin kasr 'yan Democrat su 60 suka rubutawa shugaban suna neman yayi musu afuwa saboda an shigo da yaran Amurka ba bisa ka'ida ba, da zummar wannan mataki zata hana a tusa keyarsu.
Shirin dakatar da tusa keyar irin wadannan matasa da iyayensu suka shigo da su Amurka tun suna kanana, shugaba Obama ne ya bullo da shi, wanda hakan ya baiwa matasa su dubu 740 kariya, kuma ta basu katin izinin yin aiki. Amma shugaba mai jiran gado Donald Trump, yayi alkawarin zai soke irin wadanan matakan da shugaba Obama ya dauka idan ya kama aiki.